Barka da wannan lokaci,

Jerin sunayen nan dake ƙasa na waɗanda labaransu suka yi zarra ne a gasar watan Mayun da ya gabata na shekarar da mu ke ciki mai jigo akan TA'ADDANCI.

Kamar dai yadda aka ambata tun farko za a na fidda gwarazan labarai a kowane zagaye na gasar (uku a fannin gajerun labarai sauran ukun kuma a na rubutacciyar waƙa) inda kuma za ana bayar da shaidar karramawa, shaidar lambar yabo da kuma shaidar samun damar fafatawa a gasar ga duk waɗanda suka shiga.

A ƙarshe kuma za a haɗa labarun gasannin bakiɗaya tare da wallafa su a matsayin kundin gajerun labarai na kungiyar Potiskum Writers Association (POWA).

A halin yanzu waɗannan marubutan da sunayensu ke ƙasa, su ne waɗanda labaran su suka kai izuwa matakan na ɗaya, na biyu da kuma na uku. Biye a bayan su kuma sauran waɗanda su ma suka taka rawar gani ne da maki mai yawa a ita wannan gasar.

A halin yanzu baki ɗayan su za a ba su takardun shaidar shiga wannan gasa kafin kuma wadda za a ba su a ranar babban taron bikin karramasu da kuma kaddamar da littafin gajerun labaran wadda ƙungiyar za ta shirya a kwanaki masu zuwa.

Alƙalan gasar kamar kowane lokaci sun nazarci abubuwa da dama da suka haɗa da duba kan waɗannan abubuwa:

▪Ka'idojin Rubutu 
▪Jigo
▪Warwarar Jigo
▪Salo
▪Gwanintar Harshe
▪Tsari
▪ Kiyaye Adadin Kalmomi dasauran su.

Ga kuma jerin sunayen marubutan da suka yi nasarar a fannin GAJERUN  LABARAI bisa  matakai na nasararsu daga na ɗaya kamar haka:

1. Abba Umar Yhero ----- 1st position
2. Hajiya Halima Ummi Yusuf ---- 2nd position 
3. Basira Sabo Nadabo ----- 3rd position 

Dukkan labaran da suka kai ga samun damar shiga mataki na 1 zuwa na 3 za su kasance a kundin littattafan da ake shirin bugawa na kungiyar Potiskum Writers Association (POWA) kuma kowanne daga cikin marubutan zai mallaki kwafi 5 na littafin kyauta a yayin bikin kaddamar da shi.

Sa hannu
Mahukunta.