By Hussaini Mohammed Inusa (El-hussain)

Ƙungiyar marubutan Potiskum ta gabatar da taro jiya a garin Potiskum, dake jihar Yobe. 

Yayin gabatar da taron dai an tattauna akan babutuwa da dama ciki harda batun gaggarumin babban taron da ƙungiyar ke shirin kaddamarwa wato POWASFEST inda shugaban ƙungiyar Musaddam Idriss Musa yayi bayanai da kuma jawabai masu tarin yawa kan yadda za a gudanar da bikin. 

Bayan haka an ƙaddamar da wasu matakai domin ganin bikin ya gudana yadda ake so daga ƙarshe an ji ra'ayoyin sauran jagororin ƙungiyar da suka samu damar halarta kana aka rufe taron.