Assalamu alaikum,

Barka da zuwa gasar rubutun kirkira na POWA wadda take gudana a duk karshen wata.
Jigon gasar watan nan na Agusta shi ne "NADAMA".

Ka/ki karanta wannan jawabin dake kasa tare kuma da dokokin gasar a nutse daga bisani kuma sai ka/ki rubuta gajeren labari, rubutacciyar waka ko wasan kwaikwayo akan jigon da aka ambata a sama.

Gwarzo/gwarzuwar da ya zo na daya za a ba shi/bata takardar shaidar karramawa.
Mutum biyun da labaransu suka zo matakin na biyu da na uku za a basu takardar shaidar lambar yabo. Sauran wadanda suka shiga gasar za a basu alama/shaidar samun damar fafatawa.

Za a zabi labarai hudu mafi kayatarwa tare da taskace su don bugawa a littafin gajerun labarai na kungiyar wanda za a yi shi nan gaba.

Tsarin Gasa:
1. Rubutun zai iya zama gajeren labari, wasan kwaikwayo ko rubutacciyar waka.
2. Duk rubutun da aka shigar dole ya kasance mallakin wanda ya shiga gasar ne kuma ba a taba buga shi a wani wurin ba a baya.
3. Rubutun dole ya kasance a daya daga cikin wadannan harsunan (Hausa/Turanci)
4. Gajerun labarai dole yawan kalmomin su kai 1000 kuma kar su wuce 1500.
5. Rubutacciyar waka dole ta kai baituka 20 kuma kar ta wuce baiti 50.
6. Dukkan labaran dole su kasance an yi kokarin bin ka'idojin rubutu.
7. Da labari daya kowane mutum zai shiga gasar.
8. Za a tura labarin shiga gasar ta WhatsApp a wannan lambar +2349063064582 ko kuma a +2347067132948.
9. Wadanda aka taskace labaransu za a bukaci su tura a adireshin email na kungiyar.
10. Bayan tattara labaran za a buga sunayen wadanda suka shiga gasar a shafuka da kuma zaurukan kungiyar.

Ranar rufe shiga gasa: 7 ga Satumban 2020, da misalin karfe 5:00 na yamma. 

Lokacin karbar gasar zai fara daga karfe 5:00 na yammacin yau Lahadi.

Za a fadi sakamakon a ranar/kafin ranar 17 ga Satumban 2020.

Allah ya bada sa'a. Amin