By Aisha Mohammed Sani



    _Assalamu'alaikum warahmatullahi ta'ala wa barkatuhum. Barkanmu da warhaka sannunmu da arzikin sake saduwa a  wannan lokaci na maraicen lahadi daren litinin, da ya yi dai-dai da 12/7/2020  kuma a wannan gida na powa mai cike da albarka domin gabatar da Shirin_ *BAKON POWA*

    _Shirin da yake kawo muku jajirtattun mutane daga cikin duniyar marubuta/manazarta  masu sadaukar da tunaninsu dukiyarsu  wajen ganin sun d'abbaka adabin hausa._ 

    *_Garin potiskum yau muka yi wa tsinke tare da yada zango domin lalumo bakon powa, mun samu nasara ta hanyar kak'ulo muku_  *Sulaiman Abubakar* (kawu sule) _tsohon manazarci ne fasihi mai bibiyar adabin hausa sau da k'afa._


    _Cike da dauki tare da nishadi muke gabatar muku da  da bakon mu na yau._


 *_Ku kasance tare da ni mai jan ragamar shirin;_*
      Amina ma'aji
 _(Maman kairat)_
   _Da abokan aikina;_
Aisha muhammed sani
   _(Xayyeesherth)_
Hassan bello
 _(salihi)_

 _Ku kasan ce da mu da misalin karfe takwas na dare karku sake a babu labari_

 _Maza hanzarta kataho da sauri dan ka/ki samu karuwa 'daga hirar da za mu yi_

 _da babban bakon mu kar ka/ki sake'  a baki/ka labari_

 _Mu kasan ce da ku ina muku fatan alkairi baki dayaa_

*MAI GABATARWA:*

_ASSALAMU ALAIKUM BARKAN  MU DA SA KE KASANCEWA A CIKIN SHIRIN BAK'ON POWA, MUNA YI WA BAK'ON BARKA DA ZUWA FATAN KA ISO LAFIYA?_


*BAK'O:*
Wa alaikumussalam wa Rahmatullah,
Barkanmu da wannan lokacin duk dama dai an samu jinkiri.


*MAI GABATARWA:*

Afwan za ai ma na

_DAFARKO ZA MU SO MU JI CIKAKKEN  SUNAN BAK'ON MU TARE DA TARIHIN RAYUWARSA A TAKAICE._

*BAKO:*

Bayan Gaisuwa da Girmamawa ga dukkannin illahirin Jama ar wannan Dandali mai tarin Albarka,


Da farko dai kamar yadda ya gabata Sunana *Suleiman* *Abubakar* ( *Kawu* *Sule* ),
Ni Haifaffen cikin Garin Potiskum ne, an haife ni a shekarar alif Dubu daya da dari tara da tamanin da tara  (1989).
Na fara karatu a makarantar primary ta central primary school sannan na halarci Makarantar babbar sadandari ta Jeka ka dawo cikin garin Potiskum,
Daga nan a alif Dubu biyu da tara na shiga karatu aj makarantar koyon Aikin malinta ta garin Potiskum wato Fce potiskum, inda na karanci Ilmin koyan Aikin noma wato Agricultural science Education.

Sannan Kuma bayan na kammala Karatuna na Shaidar Zama cikakken malami na fara Aiki da makaranta mai xaman kanta a matsayin Malamin aji a Alfurqan learner's academy potiskum inda ya shafe shekaru uku cur Ina koyarwa a shekakar dubu  biyu da goma Sha shida Allah ya sahhale Mana muka Bude tamu Makarantar mai Suna Premier Academy a cikin garin Potiskum din inda ya samu matsayin Headmaster daga Nan Kuma na koma Jami ar Maiduguri Don karo karatu inda na chanja sheka daga bangaren ilmi zuwa bangaren kere kere Inda nake Karatu a tsangayar Kimiyya da fasahar Noma wato Agricultural and Environmental Resources Engineering.


*MAI GABATARWA:.*

Dakyau Allah ya Kara basira.

*_TAMBAYA TA FARKO: SHIN BAK'ON  MU YA NA DA AURE NE KO KU WA YA NA NIYAR YI NE?_*

*_TAMBAYA TA BIYU: KAMAR YADDA MU KA SA NI DAI BAKON MU MAKARANCI NE SHIN ZA MU IYA SANIN ME YA JA  RA'AYIN KA KA FA RA KARANCE-KARANCE?_*


*BAKO:*
Masha Allah
Maganar  Aure kam gaskiya babu Sai dai kyakykyawar Niyya Kuma mai Karfi ma Kuma Ina bukatar Addu a da shawarwari daga gareku mutane masu daraja


Batun karance karance kuwa zance Gado nayi Don na tashi naga kakaka mahaifiyar mahaifiyata tanayi Kuma haka zalika mahaifiyata ma kawai tashi nayi na tsinci kaina a wannan lamari ,
Kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kudin Sabulu Don kuwa an ci ribar karance karance.

*MAI GABATARWA:*

🥰🥰 *DAKYAU ADDU'AR MU TA NA BIYE DA KAI A DUK IN  DA KA KE INSHA ALLAH, SHAWARWARI KU WA ANTYNMU NA NAN @Auntynmu  ZA MU BAYAR GWARGWADON  IYAWAR MU🥰*



*DAKYAU AMMAN HAKAN  YA MATUKAR BIRGENI GASKIYA🥰*

*_TAMBAYA TA UKU: KA YI KARANCE KARANCE DA DAMA KO IN CE MA KANA KAN YI, ME KA DAUKI LITTAFAN HAUSA KO IN CE WA NI KALLO KA KE YI MA SA, SANNAN SHIN KA YARDA CEWA LITTAFIN HAUSA ZAI  IYA BA TA TARBIYAR YARA MATA_*

*BAKO:*

Masha Allah To ni kam da na tsinci Abu tun daga    gida, Kinga kuwa ai zance     karance karance ya zamo limzamin ragamar tafiyar da rayuwa ta.

Hakika akwai littafan da suke Bata tarbiya Amman Basu da yawa kamar yadda ake tunani,
Kuma gaskiya ban taba ganin inda karance karance ya Zama aikin banza ba, ko ba komai Yana taimakawa wajen ha6aka ilmi da Kuma zurfin Tunani.

*MAI GABATARWA:*

Da kyau


_*TAMBAYA TA HUDU: ME ZA KA CE GAME DA MARUBUTAN BATSA? WA NI IRIN JAN HANKALI ZA KAI GARESU?*_

*BAKO:*

Fassara :

Dukkan abinda ka aikata zakaga sakamakonsa

Hakika dukkan Wanda yayi rubutun Batsa wallahi Sai yayi danasani a rayuwarsa,
Tarihi ai ya nuna dukkan masu aikata irin wadannan abubuwa sukan kasance cikin Danasani
Inaga bashi da amfani mutum ya aikata abinda zaiyi nadama Wanda daga baya in ka tuna hankalinka zai tashi Kuma fa Yana bin zuriya
Allah ya bamu ikon Aikata Alheri.

*MAI GABATARWA*
Ameen ya Allah

*_TAMBAYA TA BIYAR: SHIN BA KA DA RA'AYIN FARA RUBUTU KAMAR YADDA KA KE KARANTA NA WA SU?._*

*BAKO:*

Gaskiya Ina da muradin Farawa
Amman Kuma ai harkar tana bukatar Kwarewa da Kuma Sanin ka idojin rubutu
Insha Allah kasancewa tare daku zai taimaka min wajen ganin na cimma Burina.

*MAI GABATARWA:*

🥰 *HAKAN MA YA YI FATAN ALKAIRI, ALLAH YA SA AFARA A SA'A*.

🤦‍♀️🤦‍♀️DARE NA TAYI HAR MUN FARA WUCE LOKACIN DA A KA DIBAN  MA NA, DAN HAKA ZA MU TSAGAITA DA TAMBAYOYIN BA WAI DAN SUN KARE BA.

_*TAMBAYA TA SHIDA WA NI ABU KAI TUN NA YARINTA WANDA IN KA TUNA KO A KA TUNA MA YA KE BA KA DARIYA*_?


*BAKO:*

Don Allah Kar kumin Dariya
Abubuwa biyu ne suka kasance Dani Wanda kullum in na tuna Sai na murmusa ko Kuma in min hadu da ita wacce abin ya faru da ita

 *Na* *daya*
Akwai wacce nake so lokacin Ina College Kullum in na mata abin Alheri Sai ta fara min addu a da cewa ' :;Allah ya baka mata ta gari na dauka tana nufin ita Ashe ban sani ba an bayar da ita
 *Na* *biyu*

Muna Hira a zaunensu Wanda zai aureta yazo ya wuce mu da ya fito harda bamu kudi mu Raba Ashe Sadakinta yakai...


Wadannan abin Kullum yakan bani dariya da mamaki.

*MAI GABATARWA:*
🤭🤭🤭 *NI DAI BAN YI DARIYA BA*🤣

*TAMBAYA TA KARSHE SHIN ME ZA KA CE GAME DA WANNAN ZAUREN? SANNAN WACE SHAWARA KAKE DA ITA GA MU DA KE CIKIN TA DA MA MARUBUTA BA  KI DAYA?*.


*BAKO:*

Alhamdulillah

Gaskiya wannan dandalin shine zakaran Gwajin Dafi a dukkannin dandalin da nake dasu sabodanasamu karuwa sosai a wnnan zaure Kuma cikin ikon Allah na samu haduwa da gogaggun marubuta da Kuma Tsoffin class mates
Batun Shawara kuwa Sai dai ince  a cigaba da gashi kawai Don kuwa komai Yana tafiya bisa tsari da kwarewa.


*MAI GABATARWA:*
🥰🥰 *MASHA ALLAH MUNJI DADIN KASANCEWA DA KAI, FATAN IN MU KA KARA GYATARKA ZA KA AMSA🥰*


*BAKO:*

Nine da Godiya da kukayi haquri kuka saurareni duk da gurbacewar Hausa ta da Kuma rashin bin kaidar Rubutuna.

*MUSADDAM IDRIS MUSA:*

Muna godiya sosai sir @kawusule Allah ya kara daukaka. *A yau dai Allah ya nufa dukkan membobin POWA dake wannan dandalin sun ji amsa daga bakin mai ita game da gangaran a jerin manya-manyan mutanen da suka bayar da gudummawa wajen habbaka kungiyar Potiskum Writers Association.*

Ga wadanda ba su sani ba, Malam Suleiman shi ne ya ba wa kungiyar POWA muhalli kyauta ba haya ba, a makarantarsa ta PREMIER ACADEMY don muna gabatar da tarukan karawa juna sani da muke yi a duk karshen wata kuma zan yi amfani da wannan dama wajen sake mika godiyata a madadina da ahalin POWA baki daya zuwa gareka sir. Ubangiji ya kara lafiya, nisan kwana da arziki mai albarka, ya kuma kare mana kai daga dukkan sharri. Mun gode, mun gode. Allah ya saka da alheri.

*BAKO:*

Mune da godiya Gaskiya
Hakika kun karrama mu da ma kuka nuna Sha awar ganin kunxo Don gudanar da taro mai muhimmanci a wajenmu ,
Hakika hakan cigaba ne a wajenmu mu sauki mutane masu daraja da Kuma kokarin kawowa cigaba mai daurewa
Sannan Kuma kofa a bude take duk lokacin da Abu makamacin hakan ya taso

Allah ya Kara fiqira da Fasaha
Naji Dadi sosai
Allah ya Albarkaceku Dukkanku.

*MAI GABATARWA:*

*ALHAMDULILLAH ANAN MU KA KAWO KARSHEN WANNAN SHIRI NA MU MAI FARIN JINI TARE DA DUBIN DARASI, MU NA KARA GODIYA GAREKA YALLABAI @kawusule ALLAH YA SA KA DA ALKAIRI A HUTU GAJIYA, AMADADIN NI AISHA MOHAMMED SANI TARE DA ABOKAN AIKINA AMINA MA'AJI, HASSAN BELLO MU KE CE MU KU SAI ALLAH YA KAI MU WANI SATIN WASSALAM ALAIKUM*