SUNAN SHIRI: *Gyara Kayanka*
MAI GABATARWA: Musaddam Idriss 
LOKACI: Karfe 08:00pm
RANA: Litinin 30.03.2020
TATTARAWA: M.I Musaddam 

*Gabatarwar Shiri*

*ASSALAMU ALAIKUM*

_*Filin GYARA KAYANKA zai zo da misalin karfe 8:30 na yammacin yau kamar yadda aka saba. Kafin zuwa lokacin kuma ga wani dan gajeren labari da cikin shirin na mu ayau za mu tattauna akai*._👇

*MUTUWATA: GAJEREN LABARI*

*Farko*
Na gama fidda rai da tsammani ga samun rabo, na kuma sallamar cewa ba na daga jerin mutanen da za su yi gamo da katari na samun dace. Ban san ya ake yi ko kuma ya al'amarin yake faruwa ba illa dai kawai a ƙarshe na kan tsinci kaina tsamo-tsamo a hali na aikata laifi ko alfasha.

Kawo yanzu da na ba wa shekaru tamanin baya, ni Baba Adamu ban san yawan laifukan da na aikata ba daga zamanin da nake tashen samarta zuwa yanzu da nake kwance bisa gado na jinyar ajali, bayan da komai da na mallaka ya ƙare a wajen neman maganin cututtukan da suka yi sanadin kwanciyata har na kasance a cikin wannan hali na jinya, tun daga kan cutar dajin dana haɗu da ita a dalilin yawan shan sigari, hawan jini bisa rasa dukiya ta, cuta mai karya garkuwar jiki da na kwaso a yawon sharholiya ta da karuwai, ga ciwon ƙoda da yoyon fitsari, ban da ciwon suga da shi ma likitoci suka ce ina ɗauke da su.

Ina cikin wannan hali ne kwatsam sai ga Malam Muhammadu liman ya shigo duba lafiyata shi ne kuma kaɗai ya waiwaye ni tun bayan da na kwanta wannan jinya. Ya kuwa tarar da ni ina ta sharɓar kuka.

"Ka kwantar da hankalin ka Baba Adamu, ita cuta ai ba mutuwa ba ce, bugu da ƙari duk wanda ka ga ya kwanta jinya to Allah ne yaso shi da rahama saboda ita jinya tana kankare zunuban da mutum ya aikata ne a baya" inji liman.

Bakina na motsa daƙyar cikin jin raɗaɗin zafin ciwon dake ratsa ni nace, "Gafarta Malam...ni da na shafe tsawon rayuwa ta wajen aikata manyan laifuka ga Ubangiji ta ya ma zan kawowa kaina zaton samun rahama da har zan ɗauki wannan ciwo a irin matsayin da ka ambata...ai kawai azaba ta ce aka fara yi mani tun daga nan duniya..."

"Sam kada ka furta haka" Liman ya katse ni, "kuskure ne babba fidda rai ga samun rahamar Ubangiji. Domin kuwa Allah da kansa yana son masu tuba bisa kuskuren da suka aikata masa. Yana da kyau ka sani cewa babu wani shamaki a tsakanin mutum da mahaliccinsa kamar yadda babu hijabi ga addu'ar wanda ya tuba bisa kuskurensa. Muddin ka yi nadama akan laifukan ka to ka nemi yafiyar Ubangiji shi kuma zai gafarta maka".

Da wannan jawabi na Malam Muhammadu na samu karfin gwiwa tare da jin wani sanyi ya ratsa zuciyata saboda fahimtar girman alaƙar dake tsakanin mutum da mahaliccinsa. 

Istigifari na ci gaba da yi tare da zuba ido ina jiran ta inda *mutuwata* za ta sauko gare ni.

*Karshe!*
◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇

*Bayanin tsarin gudanar da shiri*

Shirin namu a wannan rana zai bada dama kamar yadda aka saba don yin *Sharhi, Fashin baki, tsokaci, zakulo kurakurai, jefa tambayoyi ga marubucin labarin, gami da suka ko kalubalantar rubutun (criticism)* amma kafin faruwar hakan, wannan karon za mu bi shirin ne daki-daki don gabatar da shirin a cikin tsari. 
Da fari duk wanda yake da abin fada zai fara ne da daukar lamba, Wanda yake a farko shi ne zai fara gabatar da nazarinsa kan labarin kafin mai bi masa wato tsarin nan na *first come, first serve*
1⃣
2⃣
3⃣
4⃣
5⃣
Mutane biyar shirin namu zai ba wa damar yin sharhi. Bayan kowane sharhi kuma akwai damar/yiwuwar tafka muhawara kafin a bada dama a na gaba don ya turo na shi. 

*A karshe shirin na mu, zai kammala ne da kawo mana darasi na 04 a jerin darussan mu na koyon ka'idojin rubutu.*

*Fara shirin GYARA KAYANKA*

Assalamu alaikum barkan mu da dawowa,

A wannan makon ma dai kuna tare da ni, M.I Musaddam a wani sabon filin cikin shirin mu na Gyara Kayanka inda nake dauke gare ku da wani dan takaitaccen labari mai suna *MUTUWATA*. Don ku ku yi masa taron dangi tare da kacancana shi wajen yin sharhi, tsokaci da ma gyaran kurakurai.

Lokacin daukar lambar ya yi ga duk wadanda suke a shirye daga 1 - 5.

1⃣   2⃣   3⃣   4⃣   5⃣

*A KAFTA!*

*Masu Sharhi*
Kamal Muhd Bala    1⃣
Ali Dahiru El Adi        2⃣
Hussain M. Yunusa  3⃣
Muttaka A. Hassan  4⃣

*Sharhin mai lamba ta 1⃣*
Da farko dai, wannam labarin abinda na fahimta a kai gaskiya su na da yawa. Farko dai, ana nusar da mu akan mu din ga aikata abubuwa masu kyau sannan kuma shi wanda yayi ta sharholiyar sa daga baya shiriya ta zo mi shi to kada ya cire tsammanin rahamar Ubangiji. Abubuwan suna nan da dama sosai.

*Sharhin mai lamba ta 2⃣*

*Kuskure*
Marubucin ya rubuta a cikin labarin, "Ban san ya ake yi ko ya al'amarin yake faruwa ba, illa kawai daga ƙarshe na kan tsinci kaina tsamo-tsamo a cikin hali na aikata laifi ko alfasha".

Ya za'ayi mutumin da yake aikata laifi da alfasha ace bai san ya ake hakan take faruwa ba? bayan labarin bai nuna sihiri a kai masa ba?

*Tambayar mai gabatarwa*

Shin ba ka ga cewa marubucin ya fadi hakan ne kasancewar ya bayyana mana cewa tauraron labarin ya kasance ma'abocin shan barasa wadda kuma kowa ya san cewa barasa tana gusar wa mutum da hankali ta yadda a karshe ya kan aikata abu cikin rashin sani?

*Martanin mai sharhi:*
A fahimtata duk wani mai shan giya ya san tana gusar da hankali, kenan yasan me yake sa shi aikata alfashan.

*Tambayar mai gabatarwa*

Hakan na nufin ya san illar giya cewa za ta iya kai shi ga aikata laifi kamar yadda shi da bakin shi ya fada mana kenan cewa a karshe ya kan tsinci kan shi a hali na aikata laifi. Amma kuma hakan na nufin yayin da ya bugu din ya san abinda yake aikata wan kenan ko ya abin yake?

*Martanin mai sharhi:*
Yayin da ya bugu bai san me yake aikatawa ba, amma labari ce mana ya yi, bai san ya ake yi ko kuma ya al'amarin yake faruwa ba, illa ya tsinci kansa a cikin aikata laifi da alfasha, 
ka ga kenan an nuna bai san me yake faruwa ba kawai sai dai ya tsinci kansa a cikin aikata alfasha. Saboda in dai yana cikin hankalin sa dole ya san sai ya sha giya sannan hankalin sa zai gushe har ya aikata abinda bai ma sani ba.

*Mai gabartawa*
To mun gode kwarai, lokacin ka na yin tsokaci ya cika.

Mai lamba ta 3⃣ @⁨EL HUSSAIN⁩ kawo mana abubuwan da ka nazarta game da wancan labari mai suna MUTUWATA.

*Sharhin mai lamba ta 3⃣*

*NAZARINA SHI NE:*

Wannan dan labari na dauke da darasi mai matukar muhimmanci musamman a wannan zamani da muke ciki wanda za ka ga mutane suna holewarsu kawai kai ka ce ma sun manta da cewar za su mutu kuma za a musu hisabi. 

      Labarin na dauke da babban ilimi wato sanin cewar dukkan mummunan aikin da bawa ya aikata matukar zai tuba, tuba na kwarai to tabbas Allah zai gafarta masa zunubansa.

         Sa'annan akwai izina a cikin labarin wato kada mutum ya aikata manya-manyan laifuka irin wadanda jarumin nan ya aikata domin ba dole ba ne ka aikata kuma ka samu lokacin tuba kafin mutuwarka. Ta iya yuwuwa ka mutu kana cikin aikata laifin wanda hakan zai zama babbar masifa gareka a lahira.     
        
     Bugu da Kari, kuma marucin labarin ya zo da salo na musamman kasancewar labarin dan gajere sosai amman yana dauke da abubuwa masu muhimmanci dayawa kamar su:

1. Tunatarwa
2. Fadakarwa
3. Wa'azantarwa
4. Nuni akan aikata aiyukan kwarai da dai sauransu.

*Tambayar mai gabatar wa*

Ko akwai wani guri da kake tunanin marubucin ya kuskure wajen kamar gina labarin, salon da ya yi amfani da shi, kaidojin rubutu da sauransu?

*Martanin mai lamba ta 3⃣*
To a gani na idan ma akwai kuskure bai wuce tarin cututtukan da marubucin ya zayyana a matsayin cututtukan da jarumin ya kamu da su ba a gani na sun yi masa yawa kwarai da gaske. Sa'annan kuma marubucin bai bayyana halin jarumin ba kafin ya fara holewarsa ba kuma bai bayyana abokan jarumin ba domin a al'adan ce mun san cewar abokai na da tasiri sosai wajen samun kai a cikin munanan dabi'u irin nasa.

*Tambayar mai gabatarwa*

Shin ba ka ga cewa saboda kasancewar labarin gajere ne shi yasa marubucin ya takaita bayyana wasu abubuwan? Bangaren cututtukan kuma ba ka tunanin nuni ne cikin hikima marubucin ya yi na illolin da sakamakon kowane mummunan dabi'a daga dabi'un tauraron ke haifarwa ga lafiyar wanda ya nemi tsunduma rayuwar sa a irin wannan hali?

*Martanin mai lamba ta 3⃣*
Haka ne amman mai karutu zai dauka cewar mutum daya zai yi matukar wuya ya kamu da dukkan wadancan cututtukan.

*To muna godiya, Idan lokaci ya bada dama. Za mu sake gayyatoka Kafin rufe shirin*

*Mai gabatarwa*
Mai lamba ta 4⃣ a yanzu kai muke saurare.

*Martanin mai lamba ta 4⃣*

*Zubi Da Tsari*

Tare da cewa an zubo labarin ba tare da amfani da kanun labarai ko babi ba (wataƙila saboda gajere ne), to amma labarin ya samu kyakkyawan tsari ta yadda aka yi amfani da sakin layi a wuraren da suka dace, sannan an saka ayoyi da waƙafi da sauran alamomin rubutu a inda suka dace.

*Salo Da Sarrafa Harshe*

Marubucin ya yi amfani da sassauƙan salo wurin isar da saƙonsa. A ɓangaren sarrafa harshe marubucin ya yi ƙoƙari wurin yin amfani da hikima da azanci tare da kalmomi masu sauƙi wurin isar da saƙonsa, ta yadda hatta ɗaliban ƙaramar sakandire za su iya fahimtar saƙon.

 *Warwarar Jigo*

~ Labarin na ƙoƙarin nusar da mu ba a shiga tsakanin bawa da Mahaliccinsa; komai girman laifi matsawar aka tuba Allah mai jin ƙan bayinsa ne masu tuba.

~ A fakaice labarin na tsoratar da mu a kan rashin amfani da ƙuruciyarmu yadda ta dace; kamar yadda muka ga Baba Adamu ya yi a tsufansa ya girbi gubar da ya shuka.

~ Haka kuma labarin ya nusar da mu muhimmancin ilmi, kamar yadda muka ga Malam Muhammadu (liman) ya yi amfani da ilmi ya tunatar da Baba Adamu abin da bai sani ba ko ya sani ya manta.

 *Ƙa'idojin Rubutu*

- Ya so ba yaso ba.

- Da ƙyar ba daƙyar ba.

- Da ke ba dake ba.

- Na ce ba nace ba.

- Kawo wa kaina ba kawowa kaina ba (jakada *wa* ce).

- A kan ba akan ba.

- Mahalicci ba mahalicci ba.

 *Gyara Ko Tambayoyi*

- An nuna Baba Adamu tsoho ne ɗan shekara 80, amma an lafta masa cututtuka masu haɗari rututu kamar; daji, hawan jini, ciwon ƙoda, sida da ciwon sukari. Anya kuwa waɗannan cutukan ba su yi wa dattijo mai shekaru 80 yawa ba?

- Anya dattijo ɗan shekara 80 zai iya rayuwa da waɗannan cututtuka har ma ya samu tattaunawa da mutane?

*Shawara*

- Maimakon a tara wa Baba Adamu cutuka masu yawa da haɗari har kusan biyar, zai fi kyau a ce an rage su an liƙa masa cutukan da a ɗabi'ance sukan riski tsoho mai irin shekarunsa (musamman wanda bai yi ƙuruciya mai nagarta ba) wato kamar; makanta, ciwon ƙafa, ciwon baya da sauransu.

*Tambayar mai gabatarwa*

Shin ba ka ganin cewa zaren labarin zai kubuce daga hanun marubucin ta yadda za a rasa alaka tsakanin sakamakon abinda ya girban da kuma abinda shi din ya shuka idan aka bayyana makanta ko nakasar wani sashe na jiki a maimakon ta lafiya a matsayin sakamako na wadancan munanan dabi'u musamman idan muka yi duba cewa aikata al'amura kamar shan sigari lafiyar kayan ciki yake shafa, haka shi ma bin matan banza, da shan giya duk suna shafar lafiyar cikin jiki ne maimakon waje? Idan kuma aka koma ga yawan shekarun shi, shin ba ka ga cewa marubucin ya yi la'akari da cewa akasari wadancan cututtuka suna da alaka da yawan shekaru duba da cewa a shekarun samarta garkuwar jikin Dan Adam ta kan zamo mai karfi wajen yaki da cututtuka har sai tsufa ya zo kafin kuma rauni ya shigeta ta yadda su kuma cututtukan kan bayyana karara? Ana ma iya cewa watakila marubucin ya yi amfani da batun nan ne na cewa *Allah ya na arawa mutum lokaci musamman wanda ke kan turba irin ta shi Baba Adamu wanda ke shake aya don a samu hujjar kama shi dumu-dumu a hanu?*

*Martanin mai lamba ta 4⃣*
Na gamsu. Allah Shi ƙara basira.👌🏼

*GYARA KAYANKA: Karkarewa*

Da wannan nake mika godiya ga dukkan membobin wannan zaure musamman *MASHARHANTAN MU* na yau da suka taimaka wajen zakulo mana kurakurai da ma darussan da suke cikin wannan labari mai suna MUTUWATA. Muna godiya gare ku baki daya kuma kamar yadda na ce a lokacin gabatar da shirin, kafin sauya sunan zauren zan kawo mana darasin mu na gyara kayanka

Bissalam