Barkan mu da warhaka, 

Kamar yadda aka gani a sama, wannan bayanin sunaye ne na sakamakon gasar watan Janairun da ya gabata mai taken *ZAMAN LAFIYA* wanda kungiyar Potiskum Writers Association wadda aka fi sani da (POWA) a takaice take daukar nauyi a kowane karshen wata don samar da kundi na littattafan wakoki da kuma gajerun labarai na kungiyar. Kuma kamar yadda aka karanta a jawabin da aka yi na abinda ya kawo jinkirin fitar sakamakon gasannin a wannan karo, mahukuntan da suka jagoranci alkalancin wannan waka sun yi duba ne a bisa wadannan ma'aunai wajen yin alkalancin su kamar haka:

1. JIGO: a.kwayar JIGO
               b. Warwarar JIGO
2. Zubi da Tsari:
a. Mabudi da marufi
b. Kari
c. Kafiya
d.Tsarin baiti
3. Salo da Sarrafa Harshe:
a. Luguden kalmomi
b. Azancin magana
c. Aron kalma
d. Tsarin Jumla
e. Car6in Tunanin mawaki.

A bisa wannan ma'aunai din ne muke farincikin sanar da zakarun gasar watan Janairu daga na 1 zuwa 3 wadanda suka yi nasarar shiga rukunin wadanda za a karrama su kuma a sanya ayyukan su a kundin kungiyar da ake shirin bugawa.

Gwarazan su ne kamar haka;

1. Faridat Musa (Sweery) a matsayi na 3

2. Abubakar Malam Ya'u Nguru a matsayi na 2

3. Yusuf Aminu Jibia a matsayi na 1

Za a saki sauran sakamakon gasar na wadanda suka aiko da gajerun labarai nan da wasu sa'o'i kalilan. Gobe ne kuma za a fitar da sakamakon gasar watan Fabairun da ya wuce tare kuma da sanarwar jigon shiga gasar watan Mayun da muke ciki.

Mun gode.
POWA Team