Barka da wannan lokaci,
Jerin sunayen nan na ƙasa na waɗanda labaransu suka yi zarra ne a gasar watan Janairun da ya gabata na shekarar da mu ke ciki mai taken "ZAMAN LAFIYA".

Kamar dai yadda aka ambata tun farko za a na fidda zakarun labarai guda shida a gasar kowanne wata (uku a fannin gajerun labarai sauran ukun kuma a na rubutacciyar waƙa) inda kuma za ana bayar da shaidar karramawa, shaidar lambar yabo da kuma shaidar samun damar fafatawa a gasar ga duk waɗanda suka shiga.

A halin yanzu waɗannan marubutan da sunayensu ke ƙasa, su ne waɗanda labaran su suka kai izuwa matakan na ɗaya, na biyu da kuma na uku. Biye a bayan su kuma sauran waɗanda su ma suka taka rawar gani ne da maki mai yawa a ita wannan gasar.

A halin yanzu baki ɗayan su za a ba su takardun shaidar shiga wannan gasa kafin kuma wadda za a basu da ita kuma za ta zamo ta karramawa a ranar babban bikin karramawa na ƙungiyar mai zuwa.

Alƙalan gasar kamar kowane lokaci sun nazarci abubuwa da dama da suka haɗa da duba kan waɗannan abubuwa:
▪Ka'idojin Rubutu 
▪Jigo
▪Warwarar Jigo
▪Salo
▪Gwanintar Harshe
▪Tsari
▪ Kiyaye Adadin Kalmomi dasauran su.

Ga kuma jerin sunayen marubutan da suka yi nasarar a fannin GAJERUN  LABARAI bisa  matakai na nasararsu daga na ɗaya kamar haka:

1. Rukayya Harun (Maman Nour) a matsayi na 1
2. Sadiq Shehu Sharif a matsayi na 2
3. Sakina Salisu Al-imam da kuma Mohammed Bala Garba a matsayi na 3
4. Zulaiha Haruna Rano a matsayi na 4
5. Aminullahi Lawan a matsayi na 5
Rahinat Mamoudou a matsayi na 6
5. Badiyya Adam a matsayi na 7
6. Aisha Mohammed Sani a matsayi na 8
7. Ibrahim Auwal Abubakar a matsayi na 9
8. Zainab Ahmad Yakasai a matsayi na 10
9. Bilkisu Babandede Hadejia da Amina Muhammad Inuwa (Antin Khalil) a matsayi na 11

Dukkan labaran da suka kai ga samun damar shiga mataki na 1 zuwa na 3 za su kasance a kundin littattafan da ake shirin bugawa na kungiyar Potiskum Writers Association (POWA) kuma kowanne daga cikin marubutan zai mallaki kwafi 5 na littafin kyauta a yayin bikin kaddamar da shi.

Sa hannu
POWA TEAM